بِسْمِ الله اِلرَّحْمَـنِ اِلرَّحِيمْ صَلىَّ الله عَلَى اِلنَّبِيُ اِلكَرِيمِ FIQH BABI ACIKIN RUWA Ruwa: Ruwa ya rabu gida uku : 1-Ruwa Mai Tsarki Mai Tsarkakewa (المُطلَق): Shi ne wanda launinsa ko dandanonsa ko kamshinsa bai canja ba dalilin wani abu mai najasa da ya zuba cikinsa ko marar najasa, kamar fitsari, jinni, sukari, gishiri da sauransu. Babu laifi idan kasar wurin ce ta sa ya canja. Da irin wannan ruwanne ake yin tsarki, alwala, wanka. 2-Ruwa mai tsarki marar tsarkakewa: Shi ne wanda launinsa ko dandanonsa ko kamshinsa ya canja dalilin wani abu mai tsarki da ya fada a cikinsa, kamar sukari, madara, sabulu da sauransu. Ba a yin ibada da shi, sai dai a sha, a yi wanka, a yi wanki da sauransu. 3-Ruwa mai najasa: Shi ne wanda najasa ta fada a cikinsa kuma ta sa ya canja. Kamar fitsari, giya da sauransu. Tambihi : Idan wani abu ya fada a cikin ruwa, amma bai canja masa komai ba to wannan ruwan ba shi ...
ANWARUL MUHAMMADIYYAH