Skip to main content

FIQH


  

  بِسْمِ الله اِلرَّحْمَـنِ اِلرَّحِيمْ   صَلىَّ الله عَلَى اِلنَّبِيُ اِلكَرِيمِ

FIQH

BABI ACIKIN RUWA

Ruwa: Ruwa ya rabu gida uku : 

1-Ruwa Mai Tsarki Mai Tsarkakewa (المُطلَق): Shi ne wanda launinsa ko dandanonsa ko kamshinsa bai canja ba dalilin wani abu mai najasa da ya zuba cikinsa ko marar najasa, kamar fitsari, jinni, sukari, gishiri da sauransu. Babu laifi idan kasar wurin ce ta sa ya canja. Da irin wannan ruwanne ake yin tsarki, alwala, wanka.

2-Ruwa mai tsarki marar tsarkakewa: Shi ne wanda launinsa ko dandanonsa ko kamshinsa ya canja dalilin wani abu mai tsarki da ya fada a cikinsa, kamar sukari, madara, sabulu da sauransu. Ba a yin ibada da shi, sai dai a sha, a yi wanka, a yi wanki da sauransu.

3-Ruwa mai najasa: Shi ne wanda najasa ta fada a cikinsa kuma ta sa ya canja. Kamar fitsari, giya da sauransu.

Tambihi : Idan wani abu ya fada a cikin ruwa, amma bai canja masa komai ba to wannan ruwan ba shi da matsala.

BABI ALWALA.

Alwalla: wani tsarki ne da ake yi da ruwa; ya kunshi wanke wasu kebantattun gabbai tare da niyya.

Farillanta: 1-Niyya,  2-wanke fuska,   3-wanke hannuwa zuwa guyawu,  4-shafar kai,  5-wanke kafafuwa zuwa idon sahu,  6-gaggautawa,  7-cucudawa.

Sunnoninta: 1-wanke hannaye zuwa ku`u,  2-kuskurar baki,   3-shaka ruwa,  4-fyacewa, 5- juyowa da shafuwar kai,  6-shafar kunne,   7-sabunta ruwa wurin shafar kunne,  8-jeranta farillai.

Mustahabbanta: 1-ajiye kwarya daga dama, 2-karanta ruwa, 3-goga asuwaki 4-farawa daga dama, 5-farawa daga goshi ga wanke fuska, 6-tsefe gemu sassauka, 7-tsefe yatsun kafafuwa, 8-yin Bismillah, 9-yin addua bayan gamawa 10-maimaita gabbai sau uku, 11-jeranta sunnoni.

Abin da ke warwareta: 1-bawali,  2-bayan-gari,  3-rihi,  4-gushewar hankali; ta hanyar hauka, suma, maye, bugun-aljani, barc 5-maziyyi,  6-wadiyyi 7-ridda, 8-shafar alkalami, 9-kokonto a cikin hadasi,  10-shafar mace.

Abin da bai halatta ba ga marar alwala:  Sallah, dawafi, sujadar Alkur‘ani.

Tambihi: Wanda ya manta lam`a ya wanke ta kuma ya sake sallah.

BABUN TAIMAMA

Taimama wani tsarki ne da ake yi da kasa, ya kunshi shafar fuska da hannaye kadai.

Farillanta: 1-niyya,  2-bugun-kasa na farko,  3-shafar fuska,  4-shafar hannaye zuwa ku`u,  5-shigowar lokaci,  6-wuri mai tsarki,  7-gaggautawa,  8-sadata da sallah babu jinkirtawa.

Sunnoninta: 1-shafar tsakanin ku`u da gwiwar hannu,  2-sabunta wurin bugu don shafar hannaye,  3-jeranta farillai.

Mustahabbanta: 1-yin Bismillah, 2-farawa daga dama,  3-fara shafar bayan hannu kafin cikinsa,  4-farawa daga farko.


Abin da ke Warware  Taimama

Duk abin da ke warware alwala ya na warwareta.

Tambihi: Ba`a yin sallar farilla biyu da taimama daya. Wanda ya yi sallah da taimama ya halatta ya yi nafila bayanta, da sharadin idan ya yi niyyar hakan tun da farko. Misali, wanda ya yi sallar Isha`i ya tashi ya yi shafa`i da wutiri. Ba`a yin taimama bisa tabarma,katako,ciyawa,siminti,shimfida koda akwai kura samanta.

Abin da ke sawa a yi taimama: Rashin ruwa ko rashin lafiya.

BABUN WANKA.

Wanka tsarki ne da ya kunshi wanke jiki baki dayansa da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa ba soso ba sabulu tare da niyya.

Abin da ke wajabta wanka: 1-janaba, 2-haila, 3-nifasi, 4-musuluntar kafiri.

Farillansa: 1-niyya, 2-gaggautawa, 3-cucudawa, 4-game jiki da ruwa.

Sunnoninsa: 1-wanke hannaye zuwa ku`u, 2-kuskurar baki, 3-shaka ruwa, 4-fyacewa, 5-shafar kunnuwa.

Mustahabbansa: 1-farawa da wanke najasa, 2-kama ruwa, 3-wanke gabban alwala sau guda-guda, 4-wanke kai sau uku, 5-farawa da sashen jiki na dama sannan hagu,  6-farawa da wanke sama kafin kasa, 7-karanta ruwa.

Tambihi:

Wanda ya tuna da lam`a bayan fitowarsa daga wurin wankansa, to ya gaggauta wanketa a lokacin da ya tuna ba tare da jinkiri ba, kuma ya sake dukkan sallolin da ya yi koda bayan wata ne. Idan ya jinkirta bayan tunawarsa zai sake wankan baki dayansa tare da sallolin. Idan lam`ar  tana cikin gabban alwalla kuma da ya yi alwalla ya wanke wurin to wannan ya isar masa.

BABUN JINI.

Jini da mata ke yi ya rabu zuwa uku: 1-Istihara, 2-Haila, 3- Nifasi.

Jinin Istihara: Shi ne jinin rashin lafiya, baya hana sallah ko azumi da sauransu. Mustahabbi ne ga mai yinsa ta yi alwalla kowace sallah. 

Jinin haila: Shi ne jinin da mata ke yi duk wata, baya wuce kwana (15). Mata sun kasu gida (4) a wurin haila: 1-sabon shiga ((المُبتَدَأَة , 2-wadda ta saba ( المُعتَادَة), 3-mai canjawa ( المُختَلِطَة ), 4-mai ciki ( الحَامِلُ ).

Sabon shiga : kwanakin hailarta (15) ne, idan ya dauke kafin cikarsu sai ta yi wanka, idan ya zarce (15) to ya zama na istihara.

Wadda ta saba : za ta bi yadda ta saba gani. Misali, biyar biyar,  ko takwas takwas, ko goma goma, ko sha-biyar-biyar. Idan ya zarce yadda ta saba gani zata kara masa kwana 3 matukar ba zai wuce kwana sha-biyar ba.

Mai cancanzawa : It ace wadda ta saba da haila amma bata da tsayayyar al`ada, watau duk lokacin da haila ta zo ma ta sai kwanakin sun banbanta da na baya. To idan ta ga cewa ya zarce ma ta ; za ta saurari daukewarsa zuwa mafi yawan al`adarta, in dai ba wuce kwana (15) ba.

Mai ciki : Mai ciki bata haila, amma idan ta zo mata bayan wata 3;in ta zarce yadda ta saba gani zata yi saurare har zuwa kwana (20) daga sannan ta zama mai istihara. Idan kuma ta zo ma ta ne bayan wata (6) kuma ya zarce yadda ta saba gani, za ta yi saurare har zuwa kwana (25) daga sannan ta zama mai istihara.

Nifasi: Jini ne na haihuwa ba ya wuce kwana (60). Idan ya dauke koda ranar haihuwa ne a yi wanka. Idan ya dawo bayan kwana (15) to na biyun ya zama haila idan bai kai haka ba to a hade shi da na farkon ya zama cikon sauran nifasin.

Alamomin daukewar jinni: jinni ya na da alamomin daukewa guda biyu: 

1-bushewa (الجُفُوفُ), 2-farar kassa (القَصَّةُ البَيضَاءُ)

Bushewa it ace zata yi amfani da farin kyalle ta duba taga ko akwai alamun jinni a jikinsa; idan akwai bai dauke ba idan babu ya dauke. 

Farar kassa wani ruwa ne da ke fitowa bayan bushewa.


















HUKUNCE-HUKUNCEN SHARI‘A :

Farilla/ Wajibi: Shi ne abin da ya zama dole mutum ya aikata, idan ya yi a bashi lada, idan bai yi ba a rubuta masa zunubi. Misali : Salloli (5) na rana da sauransu.

Sunna: Shi ne abin da ake so mutum ya aikata, idan ya yi a rubuta masa lada, idan bai yi ba babu zunubi sai dai asarar lada. Misali : Sallar Idi da sauransu.

Mustahabbi: Shima kamar sunna yake amma baikai sunna karfi ba, idan ya yi akwai lada, idan bai yi ba babu zunubi. Misali, aswaki wurin alwala da sauransu.

Haram: Shi ne abin da ya zama dole akan mutum ya bar shi, idan ya bari akwai lada, idan ya aikata akwai zunubi. Misali, sata da sauransu.

Makaruhi: Shi ne abin da ake so mutum ya bar shi, idan ya bari akwai lada, idan ya aikata babu zunubi. Misali, waiwaye da runtse ido duk a cikin sallah.

Halal: Shi ne abin da babu lada babu zunubi akan aikata shi ko barinsa. Misali, sanya tabarau.









BABUN SALLAH.

Sallah wata ibada ce da ta kunshi karatu kabbarori a wani kebantaccen lokaci bisa tsarin shari`a. 

Farillanta : 1-niyya 2-kabbarar harama 3-tsayuwa dominta 4-karatun fatiha 5- tsayuwa dominsa  6-ruku`u  7-dagowa daga ruku`u  8-sujada  9- dagowa 10-natsuwa  11-daidaito  12-zaman tafiya na karshe gwargwadon sallama 13-sallama  14-jeranta farillai. 

Sunnoninta: 1-ikama  2-karatun sura  3-tsayuwa dominta  4-asirtawa a muhallinta  5-bayyanawa a muhallinta  6-sami`allahu liman hamidah  7-dukkan kabbarori banda ta farko  8-tafiya  9-zaman yinta  10-gabatar da fatiha akan sura 11-sallama ta 2 da ta 3, 12-bayyana sallama ta farko  13-salati   14-sujada akan hanci  15-sanya sutra ga liman da mai sallah shi daya don gudun wucewar wani ta gabansu. 

Mustahabbanta: 1-daga hannaye ya yin kabbarar harama 2-rabbana walakalhamdu 3-cewa  amin 4-tasbihi cikin ruku`u 5-addu`a cikin sujada 6-tsawaita karatun asuba da azahar 7-gajarce karatun la`asar da magriba 8-tsakaita karatun Isha`i 9-surar farko tafi ta 2 tsawo  10-alkunut a sallar asubahi  11-addu`a bayan tahiya ta 2 kafin sallama  12-motsa yatsan hannun dama a tahiya.

Halayen sallah : Sallah ta na da halaye guda 7 da ake yin ta abisa tsarinsu. Hudu na farko jerasu farilla ne, ukun karshe kuma mustahabbi ne. 1-tsayuwa babu jingino  2-tsayuwa da jingino  3-zama babu jingino  4-zama da jingino  5-kwanciya bangaren dama  6-kwanciya bangaren hagu  7-kwanciya rigingine.

Rafkanuwa.

Sujadar rafkanuwa a cikin sallah sunna ce, ragi ya na da sujada 2 kafin sallama (kabli), kari ya na da sujada 2 bayan sallama (ba`adi). Wanda ya manta farilla ba zai yi sujada ba, don sujada kadai bata  gyara ta. Wanda ya manta mustahabbi babu laifi akansa. Ana yin sujada ne idan an rage sunna.

BABUN SUJADA KABLI

1-wanda ya manta karatun sura ya yi sujada kabli. 2-wanda ya manta kabbara 2 ka fiye da haka ya yi sujada kabli. 3-wanda ya manta ‘sami`allahu liman hamidah’ sau 2 ko fiye da haka ya yi sujada kabli. 4-wanda ya manta zama na farko ya yi sujada kabli. 5-wanda ya boye karatu inda ake bayyanawa ya yi sujada kabli. 6-wanda ya manta karatun tahiya ya yi sujada kabli. 7-wanda ya yi ragi kuma ya yi kari ya yi sujada kabli.

SUJADA BA`ADI:

1-wanda ya kara raka`a da mantuwa ya yi sujada ba`adi. 2-wanda ya bayyana karatu inda ake asirtawa ya yi sujada ba`adi. 3-wanda ya yi sallama a raka`a ta 2 ya yi sujada ba`adi. 4-wanda ya zauna a raka`a ta farko ko ta uku ya yib sujada ba`adi. 5-wanda ya yi Magana cikin mantuwa ya yi sujada ba`adi. 6-Wanda ya yi kaari a cikin karatunsa ya fadi kalmar da babu ita a cikin Alkur`ani ya yi sujada ba`adi. 7-Wanda ya maimaita fatiha da mantuwa ya yi sujada ba`adi.

Zikirori bayan gama sallah: wanda ya gama sallah zai karanta:

ASTAGFIRULLAH SAU UKU أستغفر الله  (3)

ALLAHUMMA ANTAS SALAAMU WAMINKAS SALAAM TABARAKTA YAA ZAL JALAALI WAL IKRAAM        
اللهم أنت السلام و منك السلام تباركت يا ذا الجلال و الإكرام

3.  SUBHAANAL LAH SAU TALATIN DA UKU
سبحان الله (33)                                             

4. WALHAMDU LILLAH SAUTALATIN DA UKU والحمد لله (33)

5. WALLAHU AKBAR SAUTALATIN DA UKU والله أكبر (33)

6. LAA ILAAHA ILLALLAHU WA HDAHU LAA SHARII KALAHU LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU BIYADIHIL KHAIRU WA HUWA ALAA KULLI SHAI’IN KADIIR.

ـ لا إله إلا الله وحده لا شريك له له الملك و له الحمد بيده الخير و هو على كل شيئ قدير.

ـ اللهم ـ عني على ذكرك و شكرك و حُسن عبادتك.7.  ـ 

آية الكرسيّ 8. AAYATULKURSI
الصلاة على النبي صلى الله عليه و سلم      9. SALATI GA ANNABI (SAW)   10. ADDU’O’I

















BABUN AZUMI

MAANAR AZUMI

Imam An-Nawawiy da Ibn Hajar Sun fassara Azumi da; Kamewa ko barin wasu abubuwa Kebantattu, a wani zamani kebantacce, da wasu sharudda kebantattu.

Azumi ya kunshi rashin cin abinci da shan abin sha da saduwa (Jimai) da kamewa daga karya, tun daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana da niyyar bauta wa Allah. Bukhari

Azumi ya kasu gida biyu 1. Azumin farilla da 2. Azumin Nafila

1. Azumin farilla 

shine azumin da Allah  (SWA) ya faralanta ma bawa tsawon wata daya (kwana 29 ko 30) a jere, sau daya a cikin shekara.

Maanar Ramadana a kalmar Larabci shine tsananin zafi. Shi ya sa wasu malaman suke ganin ba zaa ce kayi azumin Ramadana ba. Don haka Imamul Bukhari ya kulla babi da ke nuna babu laifi don ka ce ka yi azumin Ramadana.

Kuma azumi shi ne kamewa daga cin abinci da sha da saduwa tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana domin neman kusanci ga Allah. Allah Yana cewa Ku ci ku sha har sai farin zare (alfijir) ya bayyana gare ku daga bakin zare (duhun dare)  Sahihul Bukhari 187


WAJABCIN AZUMIN RAMADANA

An wajabta azumin Ramadana ne a cikin shekara ta biyu bayan hijirar manzon Allah sallallahu alaihi waalihi wasallam daga Makka zuwa Madina, Allah mai girma da daukaka ya saukar da wajabcin Azumi ne cikin watan Shaaban shekara ta biyu bayan hijira. {Fiqhu ala mazahibul Arbaa da Nayl Al-Awwatar ash- shaukhany}

 Manzon Allah sallallahu alayhi waalihi wasallam ya yi azumin Ramadana na tsawon shekara tara a rayuwarsa, cikin watan Shaaban shekara ta biyu bayan hijirar sa, sallahu alaihi wa,alihi wasallam. ‏[Fatawaa Imamin Nawawi 152 da Zadul Ma’ad 2/26]

Allah (SWA) ya ce "Ya ku wadanda kuka yi imani, an wajabta maku yin azumi kamar yadda aka wajbta ma wadanda suka wuce kafin ku, domin ku sami tsoron Allah…. Ranaku [kwanuka] ne kididdigaggu (iyakanttatu) [Bakara 183-183]

Manzon Allah sallallahu alayhi waalihi wasallam ya ce, An gina musulunci a kan Rukunai guda biyar: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi manzon Allah ne, da tsayar da Sallah, da ba da Zakka, da aikin Hajji da Azumin watan Ramadan. [Bukhari hadisi 63]

ASALIN AZUMIN WATAN RAMADANA

Asalin azumin Ramadana ba dole ba ne, Wanda ya keda iko ya yi, wanda kuma ya so ya ciyar; kuma a wancan lokacin kwana uku a ke yi. Daga baya Allah ya mayar da shi wajibi. [Zadul Maad 29/2]

Alummar da suka wuce kafin mu tun daga zamanin Annabi Nuhu har ya zuwa farkon zamanin Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Azumin kwana uku su ke yi a kowane wata. Amma daga zamanin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Allah ya wajabbata shi a kan kowane musulmi. [Tafsirul Ibn Kasir]

Tambihi

Wanda ya ki yin Azumi ko ya fara ya karya da gangan ba da wata laluraba, Ya aikata babban laifi da ya zama wajibi ya tuba. Manzon Allah (SAW) ya fadi cewa ya ga wadansu mutane a cikin mafarki an rataye su daga Makyangyamar su, gefen bakunansu sun barke suna zubar da jini. Da ya yi tambaya game da su, sai aka shaida ma shi cewa su ne wadanda ke cin abinci kafin lokaci ya yi a cikin ramadhaana (Buda Baki), don haka ba su zamo masu yin azumi ba, saboda suna karya shi kafin lokacin shan ruwa ya yi. [Sahihu Targhib wattarhib Imamul Munzir 1005].

Sashen Malamai suka ce: tabbataccen abu ne a wurin muminai cewa duk wanda ya ki yin azumin watan Ramadan ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, (Kamar rashin lafiya, tsufa, tafiya da tsoron halaka) wannan mutum ya fi mazinaci da mashayin giya muni, kuma ana shakkar musuluncinsa, kuma ana yi masa kallon Zindiki, kuma halakakke.

FALALAR AZUMI

 Azumi garkuwa ce daga wuta, (yana kare wanda ya yi shi daga shiga wuta)

 Azumi zai yi ceto ga Wanda yake yinsa

 Ana tanadarwa mai Azumi gafara da lada mai yawa wadda ba ta da iyaka

 Azumi na shigar da mai yin sa Aljanna

 Azumi na taimakawa wajen samun tsoron Allah

Wanda ya yi Azumi rana daya domin Allah, Allah zai nisantar da shi daga wuta na tsawon tafiyar shekara sabain.

 Akwai kofa a Aljanna mai suna Rayyan wanda masu azumi ne kawai za su bi ta cikinta lokacin shiga Aljanna.

Wanda ya yi azumin Ramadan yana mai imani, Allah ya gafarta masa zunubansa.

 Malaiku suna roka wa mai azumi gafara har zuwa shan ruwa.

 Ana gafarta wa mai Azumi a karshen watan Ramadan.

 Azumi yana maganin cututtuka masu yawa.

 Azumi na kara lafiya ga mai yinsa da sauran su.


GANIN WATA

Imamul allama ashaykh Abdulbari aslishmawiy Arufaaiy ya fada a cikin littafinsa Ishmawiy yace: Ana fara Azumin Ramadan ne saboda cikar watan Shauwal, ko kuma saboda ganin watan adilai ko jamaa (yawan Jamaa).


Saboda haka, ana fara Azumi ne daga ranar da aka ga jinjirin watan Ramadan. Kuma ana shan ruwa yayin da aka ga jinjirin watan shawwal ko kuma cikar watan Shaaban kwana talatin (30). Idan watan shaaban ya kai kwana talatin ko ba a ga wata ba za a tashi da Azumi domin watan musulunci ba ya wuce kwana talatin, haka hadisi ya tabbatar. Kamar yadda yazo a cikin Bukhari da Muslim.

FADAKARWA:


Ba a yarda a yi anfani da hisabi na taurari ko kalanda ba wajen daukan azumi ko ajewa ba, Abin da Annabi sallallahu alaihi waaihiwasallam ya umurce mu shi ne ganin wata kuru-kuru da idanu bata hanyar hisabi ko kalanda ba, Annabi sallallahu alaihi waaihiwasallam yayi hani da yin amfani da hisabi  kamar yadda hadisin Imam Musulim ya nuna idan mutune adilai suka ga wata, za a yi azumi, za kuma a a jiye azumi.  

Hakanan Bayhakee da Abu Dauda sun ruwaito hadisi da isnadin su har zuwa kan Sayyidina Abdullahi Ibn Umar Allah ya kara masu yarda, Sayyidina Abdullahi ya shaida ma Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi cewa ya ga watan azumi, Manzon Allah ya yi azumin, kuma ya ba da Umurni da a yi azumin.

Da yawan malamai suna ganin cewa ana daukar azumi saboda ganin Jamaa adilai amma ba mutun daya tak ba, Allah ne Masani.

Haka nan idan wani gari suka ga watan Ramadan ko shawwal, to sauran garuruwan da suka samu labari suma za dauki azumi kuma za su aje.

Saboda halin da ake ciki na fahimata daban daban, Mutun zai yi aiki ne da Hadisin Imam Hassan jikan Annabi (SAW) wanda Imam Nawawi ya fitar cewa kabar abinda kake kokwanto ka koma ma wanda baka kokwanto.



NlYYA

Wajibi ne ka daura niyyar yin azumin Ramadan tun kafin fitowar Alfijir; Hakan, baya hallata a yi niyar azumi kafin ganin wata.

Wanda bai ga wata ba kuma bai samu labarin ganin wata har sai bayan alfijir, to ya wajaba ya kame bakin sa, kuma babu makawa sai ya rama azumin ranar saboda rashin Niyya. Kamar yadda ya tabbata daga  Hadisin Sayyidatuna Hafat (R.A) daga Manzon Allah (saw) yace: Wanda  bai niyar azumi ba kafin alfijir, baya da azumi (Imamu Ahmad, Hudu, ibn Khuzaima, Ibn Hibbaan da Darukudni).


BUDE-BAKI

Ana bude baki ne da zarar rana ta fadi (taboyu), Anso a gaggauta yin buda baki. Saboda Hadisin day a gabata.

Ana son mai azumi ya yi addua yayin

Shan ruwa (Buda Baki).  adduar kuwa ita ce: 

ذهب الظماء وبتلت عرق وثبت الأجر إنشاء الله 

"Zahabaaz zama’u wabtalatil uruku wathabbatal ajru insha Allah” [Abu Daud 2357 da Nisa’i fil Kabir10131-339]

Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, Mutane ba su gushe ba suna cikin alheri matukar suna gaggauta buda baki [Bukhari]·


FAIDA

 Ana dai son mutum ya sha ruwa ne da zarar rana ta fadi (Dare yayi).

Anso mutum ya sha ruwa [bude-bakinsa] da Dabino danye in hakan ya samu. In kuma bai samu ba ya sha ruwa, da yayan itace, kamar Kankana, Lemu, Mangwaro, Ayaba da dai sauransu in yana da iko.

Fadakarwa:

Ya kamata muyi taka tsantsan da wannan zamani a wajan gaggauta buda baki saboda hadisin da gabata cewa Manzon Allah (SAW) ya ga wadansu mutane a cikin mafarki an rataye su daga Makyangyamar su, gefen bakunansu sun barke suna zubar da jini. Da ya yi tambaya game da su, sai aka shaida ma shi cewa su ne wadanda ke cin abinci kafin lokaci ya yi a cikin ramadhaana (Buda Baki).


HUKUNCE-HUKUNCEN AZUMI


WADANDA AZUMI YA ZAMA DOLE A KANSU


Wanda Azumi ya zama dole a kansu su ne;

1. Musulmi banda kafiri.

2. Baligi banda yaro, azumi bai za ma dole ba a kan yaro

3. Mai hankali banda Mahaukaci.

4. Mai lafiya banda mara lafiya.

5. Mazauni banda matafiyi.

6. Yankewar jinin haila banda masu yin haila.

7. Yankewar jinin haihuwa banda masu jinin biki. 


WADANDA BA ZA SU YI AZUMI BA AMMA ZA SU RAMA

1.  Matafiyi wanda ya isa yin kasaru 2. Mai haila 3. Mai jinin haihuwa 4. Marallafiya (Da sauran su)


WADANDA BA ZA SU YI AZUMI BA, BA KUMA ZA SU RAMA BA SAI DAI CIYARWA

Tsoho wanda ya tsufa sosai: kamar yadda Imam Bukhari yafitar daga Sayyidina Abullahi Ibn Abbas Allah ya kara masa yarda ya ce tsoho babba da mace tsohuwa wadanda ba sa iya azumi sai su ciyar da miskini guda daya kowace rana. [Bukhari]

Haka nan Darukunni yafitar daga  Sayyidina Abu Huraira (R.A) ya ce kullum sai su ciyar da mudu guda daya na alkama. 

Haka nan Sayyidina Anas (R.A) shi ma da ya manyan ta ciyarwa ya rika yi ba ya Azumi. [Darukunni]

Wanda ke fama da rashin lafiya mai tsanani kuma ya yanke kaunar warkewarsa, misali ciwon gyambon ciki ULCERwanda ba ya iya dadewa bai ci abinci ba kuma bazai iya ramawa ba bayyan Ramadana, to shima ciyarwa zai yi ba azumi ba. Da sauransu.


ABUBUWAN DA BA SA KARYA AZUMI

1. Kwana da janaba a jiki. 2. Kurkure` baki da shaka ruwa. 4. Fitar maniyyi ta mafarki da rana 5. Yin kaho, amma anki ayi saboda tsoran tagayyara 6. Zuba ruwa mai sanyi a fuska ko a kai. 7. Dandana abinci amma a tofar bayan dandanawar. 8. Amai ba da gangan ba. Da makamantan su. 9. Yankewar jinin Haila ko Haihuwa, ko da baza asami damar yin wanka har sai bayan alfijir. Da makaman tan su.

ABUBUWAN DA KE KARYA AZUMI

1. JimaI 2. Zuwan Jinin Haila 3. Cin abinci da gangan. 4. Yin amai da gangan. 5. Zuwan jinin haihuwa 6. Gogoto. Da makaman tan su

FADAKARWA; Wanda ya aikata daya daga cikin waddanan da ke sama da gangan, ramuwa da kaffara ta wajaba akansa.


YIN SAHUR

Ba dole ba ne mutun ya cika cikinsa da abinci lokacin sahur ba, ruwa, fura, dabino ko abinda Allah (SayyidinaW.A) ya sawake masa ma ya isa. Ana so a jinkirta sahur ya zuwa juzui na karshen dare matukar alfijir bai fito ba. Hakanan, ya zama dole Idan Alfijr ya fito a dena cin.

Yin sahur sunna ce mai karfi, Manzon Allah Sallallahu Alayhi Wasallam yace: “Banbancin Azuminmu da na Yawudawa da Nasara (Kiristoci) shi ne yin sahur.  

Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, Ku yi sahur ko da da kurbar ruwa ne [Ibn Hibban]

Yazo a cikin hadisin Abu Dauda da Ibn Hibban Annabi (S.A.W) ya ce, Madalla da sahur din mumini da ya yi da Dabino

ABUBUWAN DA AKE SO A YAWAITA SU A RAMADAN

1. Yawaita karatun Alkuran.

2. Yawaita Salati ga Annabi (SayyidinaA.W) 

3. Yawaita neman gafara (Istigifari).

4. Yin sallar dare.(Tarawihi da Tahajjudi)

5. Shiga itikafi.

6. Yawaita kyauta

7. Sadaka.

8. Zuwa wajen waazi.

9. Yawaita tuba ga Allah (SayyidinaW.A).

10. Ciyar da abinci dafaffe da danye.

11. Tufatar da Muslmi. Da Sauransu.


ABUBUWAN DA YA KAMATA MAI AZUMI YA NISANTA DASU;

Kallon duk wani a bin da Allah ya haramta, da nisantar sa

Zuwa kallon kwallo: Bai halarsta gaa mai azumi ya je ya kalle su ba, domin kallon kwallo haramun ne, ko bakomai akwai nuna tsiraici kamar fitar da cinya wanda bai halatta ba ga namiji da mace.

"Manzon Allah ya ce cinya tana daga alaura. Haka ya gaya wa wani mutumi da ya fitar da cinyarsa. Sai ya ce masa, Rufe cinyarka domin cinya tana da ga alaura". [Ahmad]

Shangiya (dare ko rana), 58 Dara da caca Allah ya hana su a cikin suratul Maida su ma haramun ne ga mai azumi da ma wanda ba ya azumi. 

Hira da yammata

Mayar da dare ya zama rana. (Dogon hira) batare da dalili ba kamar masu Sanaa Teloli da sauran su

Yin barci har lokacin salla ya wuce da gangan.

Almubazzaranci wajen cin abinci.

Yin sahur da wuri, kuma a koma a yi barci har lokacin sallar asuba ya wuce.

Kin yin sallar Tarawihi.


FADAKAR WA

Ya kamata mai azumi ya himman tu da rokon Gafarar Allah da Aljanna, domin Allah ya kebanci Ramadan da alkhairai kamar haka:

Malaiku na roka wa mai azumi gafara har ya yi buda baki.

Warin bakin mai azumi ya fi kamshin turaren miski a wajen Allah.

Ana daure shedanu.

Ana bubbude kofofin Aljanna a kuma rufe kofofin wuta.

Daren Lailatul Kadri.

Allah yana gafarta zunubban bayi a cikin ramadana.


YIN UMRA A CIKIN WATAN RAMADANA

A nason yin Umra acikin Ramadan, domin hakika Umra tana daga cikin manya-manyan ayukka da ke da tarin lada mai yawa a wajen Allah musamman a cikin Ramadan. An samo hadisi  daga Sayyidina Abdullahi Ibn Abbas Allah ya kara masa yarda ya ce,  Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, yin Umura a cikin ramadana kamar ka yi aikin Hajji tare da ni ne. (wato tare da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) [Bukhari da Muslim] .

TARAWIHI (ASHAM)

Ita dai Tarawihi/Asham nafila ce, amma mutane sunfi kebantar ta acikin watan Ramadan bayan Sallar Ishai kadai. Hakika, mutum ya sallace ta gida ya fi lada da ya yi ta a masallaci amma banda na watan Ramadan domin yinta a cikin Jami yafi lada.

Manzon Allah (S.A.W) ya yi sallar tarawihi sau uku a cikin jami, daga baya ya bari saboda tsoron kar a wajabta ta a kan al-ummarsa [Bukhari da Musulim].

FADAKARWA

Sallar Tarawihi a cikin Jam'i tana da asali, domin Annabi sallahu alaihi waalihi wasallam ya yi, kamar yadda muka gani a hadisin da ke sama,

Da yawan Malamai su na ganin yin Sallar Tarawihi a Masallaci shi yafi lada, hujjar su ita ce hadisin da ya ce Wanda ya yi sallar dare tare da limami har ya gama za a rubuta mai ladan ya sallaci daren ne baki daya (Ibn Kudamah 607/2).

Amma a wurin Imam Malik yana ganin ka yi Sallar Tarawihin a gida ya fi, shi yasa ma yake yin sallar Tarawihin sa a gida, dogaransa da maganar Annabi sallallahu alaihi waalihi wasallam da ya ke cewa Mafificiyar sallar mutum wanda ya yi a gida sai dai in ta farilla ce wannan itace hujjarsa.  Ta iya yi yuwa Imam Malik yana ganin hadisin Ibn Kudamah (wanda ke sama) yana maga ne a kan Sallar Tahajjudi ba tarawihi ba, kamar yadda zaizo a gaba a cikin babin da ke Magana a kan yin Sallar Tahajjudi bayan Sallar tarawihi. Allah ne Masani.

Shehu Usmanu ibn Fodio ya bayyana Sallar Tarawihi cikin Jami a matsayin bidia maikyau saboda Sayyidina Umar (R.A) ya raya ta cikin jami. Ammakuma ya ambabace ta da bidia, Shehu Usmanu ya ci gaba da cewa da Sayyidina Umar (RA) bai kirata da bidia ba da ta zamo Sunna. (Ihyaaussunnah)

ADADIN RAKAOIN SALLAR TARAWIHI

An samu ruwayoyi da dama akan adadin raka'o'in Sallar tarawihi Amma mu a yan kinmu na magbrib rakaa goma sha uku ce duk da shafa'i da wutiri, do garo da Hadisin da Abu zaid al Kiyrawani ya kawo a cikin littafinsa Risala daga Nana Aisha Allah ya kara mata yarda, wanda yake nuna cewa Manzon Allah (SAW) na yin rakaa goma sha uku,

ZUWAN MATA MASALLACI DON GABATAR DA SALLAR TARAWIHI

Ya halatta su ma mata su bi sallar tarawihi a cikin jam'i. Saboda Hadisai masu yawa sun zo kan zuwan mata masallaci don sallar Tarawihi ko Tahajjud.  Sayyidina Umar Allah ya kara masa yarda ya sanya limamai guda biyu : Sayyidina Ubayyi ibn Kaab da Tamimud Dari, daya na ma maza limanci daya nama mata. Kuma duk sallar da ake yi mata na halarta, kuma rakaa goma sha daya suke yi [Muwatta].

Amma Mace tayi tarawihi ko tahjudi acikin gidan ta shi yafi alheri da taje Masallaci domin Hadisi ya tabbata cewa mace ko a Makka ta ke ko Madina tayi a gida yafi da taje masallaci.

Hadisi ya tabbata Ummu Humaidi ta zo wajen Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ta ce  Ina son in rikayin sallah tare da kai a masallacin ka sai Manzon sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya ce mata  Nasan kina son ki sallah tare dani to amma ki yi sallarki a dakin ki ya fi maki alheri da kiyi sallah a masallaci. [Ahmad 6/371 da ibn Khuzaimah 3/95].

SA MA MATA  LIMAMI

Ba bu laifi in an sa ma mata na su limamin na masammam in masallacin yana da fadi da tsawo mu na iya cewa yin haka ma shi ya fi dacewa saboda halin da muke ciki, kuma ya tabbata Nana Aisha Allah ya kara mata yarda tana da wanda tasa ya ke yi ma mata sallah (limanci) ita da sauran mata suna binsa, kuma zamanin Sayyidina Umar Allah ya kara masa yarda ya kasance ya sanya ma mata Sayyidina Sulaiman bn Hasmah ya yi wa mata limanci a sallar Tarawihi. 

Sayyidina Aliyu (Allah ya kara masa yarda) shima ya kasance ya na umurtan mutane da yin sallar Tarawihi shine kuma wanda ya ke ma mata limanci.

Wanda Sayyidina Umar ya sanya ya rika yin ma mata limanci shine Sulaiman bn Abi Hasmah, su kuma maza babban sahabi Annabi, mahaddacin Kurani Sayyidina Ubayu bn Kaab Allah ya kara yarda da shi.

Wannan ya nuna cewa mace bazata yi limanci ba, kuma babu laifi wani masani ya jagoran ci matan Unguwa ko gari Sallar tarawihi ko Tahajjud. Amma suyi agida shi yafi lada da daraja da suje masallaci ya kamata mata su gane cewa sallar su a uwar dakin su yafi lada da tayi a falo, haka ya tabbata a hadisi. Kamar yadda yazo acikin littafin Attamhid na ibn AbdulBar 23/398.


YIN TAHAJJUD BAYAN TARAAWIHI (ASHAM) DA KUMA YIN TA A CIKIN JAMI


Amma in ka duba Bugyatul Mutadawii ya hada hadisan duka ya yi bayaninsu (wadanda suka gabata a cikin babin tarawihi a wurin fadakarwa). Don haka idan mutum yayi sallar tarawihi ba zai yi tuhajjidi ba sai dai in ya tashi ya karanta Al-Kurani. 


Wasu malaman kuma sun ce zai iya yi matukar bai yi wuturi ba amma in ya yi wuturi ba zai yi ba domin Tahajjudi sai bayan an yi barci an farka ake yinta.


Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi wata rana da daddare ya shigo masallaci sai yaga mutane a karshen masallaci sai ya yi tambaya ya ce wadancan me su keyi sai mai Magana ya ce mutane ne basu da hadda Kurani

Ubay bn Kaab yake masu limanci sai Annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallam ya ce sun dace kuma sun kyauta. [Baihaki]

Imam Ahmad bn Hambal yana yin sallar Tahajjud ne a masallaci yana bin limami har sai angama sallah saboda ya sami ladan da Annabi sallallahu alaihi waalihi wasallam ya fada na ladan wanda yabi liman sallar dare har ya gama, Malamai dai sun rinjaya a kan yin sallar Tahajjudi a masallaci ya fida lada da kayi kai kadai a gida, wallahu aalam.


 

ADADIN RAKAOIN SALLAR TAHAJJUD/KIYAMUL LAIL


Ibn AbdulBar a cikin littafinsa Attamhid ya ce ba bu sabani tsakanin musulmai cewa sallar dare ba ta da adadi kayyadadde domin nafila ce, aiki ne na alheri, wanda ya so ya takaita wanda ya so ya yawaita [Attamhid].


BUDE KURANI

Ya halasta a bude Kurani wajen sallar Tarawihi ko Tahajjudi idan anrasa Mahaddaci, amma ba kowa zai bude ba sai dai Limami ne kawai zai bude banda sauran mamu.

Yazo a cikin Muwadda da Sahihul Bukhari wanada aka samu ta hannun Nana Aisha Allah ya kara yarda da ita ta sa wani bawa nata mai suna Zakwan yana masu sallar Tarawihi yana bude kurani yana karantawa, amma su Nana Aisha da sauran mamu ba su bude ba.

SAUKE KURANI A CIKIN SALLAR TARAWIHI KO SALLAR DARE (TAHAJJUDI)

Manzan Allah sallallahu alaihi waalihi bai kaiyede iya ayoyin da mutum zai karanta ba a sallar dare ko (Tahajjudi) ko Tarawihi, sai dai shi manzon Allah sallallahu alaihi waalihi wasalam ya kasance ya kan tsawaita wani lokaci wani lokaci kuma ya takaita ya tabbata wani dare ya yi sallah da surori mafiya tsawo acikin Kurani Bakara da AliImirana da Nisai da Maidah da Anam da Aaraf da Tauba  a cikin dare daya kuma alhalin bai da lafiya.

Kuma wani dare yayi sallah ya karanta Bakara da Nisai da Ali-Imirana a rakaa daya kuma yana karantunsa a hankali.

Kuma ya tabbata lokacin da sahabi Umar ya sanya Sayyidina Ubayu bn Kaab yana ma sahabbai limancin sallar Tarawihi/Tajjudi ya kasance yana karanta aya 200 har mutane suna dogara da sanda sabo da dadewa yana sallah, basa gamawa sai gaf da alfijir

Don haka ya danganta ga masu bin limamin ne in za su iya dadewa suna sallar to ana iya dadewa, hakanan ma in zasu iya sauke kuranin ba tare da an kuntata ma kowa ba to ana iya yi amma ba dole ne sai an sauke Kurani ba, don ya tabbata manzon Allah sallallahu alaihi waalihi wasallam ya yi sallah da aya daya.

Ansamu da ga magabata suna sauke kurani a sallar Tarawihi/Tahajjudi kamar: 

Imamu Katadah ya kasance yana sauke kurani a cikin kwana uku a sallarsa a farkon Ramadana amma a goman karshe kullun dare ya ke saukewa a cikin sallah amma fa shi kade ya ke yin sallarsa.

A mazahabar Imam Hambila da Imam Shafii da ruwaya da a kasamo daga al-Hassan da ga Abu Hanifa cewa sunna ne a sauke Kurani gaba dayansa a cikin sallar Tarawihi/Tahajjudi sabo da jamaa su ji karatun Kurani gaba dayansa a cikin sallah. Mazahabar Hanafiya su kuma su ka ce a sauke sau daya.

Abu Dawood ya ce an tambayi Ahmad ibn Hanbal game da mutumin da ya ke sauke kurani sau biyu a cikin sallah sai ya ce ya danganta ne ga mutanen da suke binsa ko suna da karfin da za su iya ko kuwa a kwai maaikata a cikinsu.

Ibn Rajab al-Hanbali ya ce maganar Imam Ahmad ta nuna mana liman ya lura da masu binsa kada ya kuntata masu ko ya koresu ya hana su zuwa wannan ita ce fahintar wasu da ga cikin mazahabar Hanafiya.

ADDUAR KUNUTI

Alqunut tana dakyau a cikin Tahajjud. Ana yin tane bayan an gama karatun Kurani a rakaar karshe  sai ayi addua kafin a je ruku'o. Kamar yadda ya tabbata daga Manzon Allah sallallahu alaihi waalihi wasalam ya na yi har ma ya koya ma jikansa Al Hassan bn Ali adduar da zai rika karantawa a cikin alkunutinsa. Hakan  babu laifi in ansa adduar Kunutin bayan an dago daga rukuo. Lafazin adduar shine:

" ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻫﺪﻧﻲ ﻓﻴﻤﻦ ﻫﺪﻳﺖ ﻭﻋﺎﻓﻨﻲ ﻓﻴﻤﻦ

ﻋﺎﻓﻴﺖ ﻭﺗﻮﻟﻨﻲ ﻓﻴﻤﻦ ﺗﻮﻟﻴﺖ ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻟﻲ ﻓﻴﻤﺎ

ﺃﻋﻄﻴﺖ ﻭﻗﻨﻲ ﺷﺮ ﻣﺎ ﻗﻀﻴﺖ ﻓﺈﻧﻚ ﺗﻘﻀﻲ ﻭﻻ

ﻳﻘﻀﻰ ﻋﻠﻴﻚ ﻭﺇﻧﻪ ﻻ ﻳﺬﻝ ﻣﻦ ﻭﺍﻟﻴﺖ ﻭﻻ ﻳﻌﺰ ﻣﻦ

ﻋﺎﺩﻳﺖ ﺗﺒﺎﺭﻛﺖ ﺭﺑﻨﺎ ﻭﺗﻌﺎﻟﻴﺖ ﻻ ﻣﻨﺠﺎ ﻣﻨﻚ ﺇﻻ

ﺇﻟﻴﻚ

Daga nan sai kai ma Annabi sallallahu alaihi waalihi wasalam salati kuma kai ma sauran musulmai addua ta alkhairi sannan aima kafire mummunar addua.

ZIKIRIN DA AKE KARANTAWA BAYAN ANGAMA TARAWIHI /TAHAJJUDI

Ya tabbata cewa bayan ka gama sallar dare bayan kayi wuturi a kwai zikirin da zaka karanta sau uku(3) sau biyu ahankali na ukun sai ka daga muryarka da karfi ka karanta, zikirin kuwa shi ne.

سبحان ملك القدس * سبحان ملك القدس** سبحان ملك القدس** 

SUBHANAL MALIKIL KUDDUS, SUBHANAL MALIKIL KUDDUS SUBHANAL MALIKIL KUDDUS [Sahih Abi Duaud 1284].

I’ITIKAFI

I’itikafi na nufin, lazimtar wani abu da kuma tsayar da rai a kanshi. Ma’anar I’itikafi a shariance ta kunshi zama a Masallaci don yin ibada cikin wata siffa kebantacciya, kuma cikin wata kama kebantacciya.

Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana yin iitikafi na kwana goma amma a shekarar da yai wafati ya yi na kwana ashirin. [Bukhari da Muslim].

Kai ma za ka iya yin na kwana ashirin. Ana yin iitikafi ne a cikin masallaci kamar yadda Allah ya fada a cikin suratul Bakara.

Amma dai an fi so a yi shi a kwanukan goman karshe na Ramadana kamar yadda sunna ta bayyanar.

ﻭﻻ ﺗﺒﺎﺷﺮﻭﻫﻦ ﻭﺃﻧﺘﻢ ﻋﺎﻛﻔﻮﻥ ﻓﻲ

ﺍﻟﻤﺴﺎﺟﺪ

1. Ana iya yin i’itikafi a kowane lokaci. Hadisi ya tabbatar cewa Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi i’itikafi a cikin watan shawwal [Bukhari]. An fi so a yi shi a kwanukan goman karshe na Ramadana kamar yadda sunna ta bayyanar, kamar yadda ya gaba ta.

2. Iitikafi sunna ce mai karfi daga cikin sunnonin da Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam ya dawwama yana aikatawa. Tun da Annabi ya fara iitikafi bai bari ba har ya bar duniya kuma bayansa matayensa sun cigaba da yin iitikafi [108] .

3. Imam Muhammad ibn Shihabuz Zuhri ya ce game da falalar iitikafi; Abin mamaki yadda mutane su ke barin iitikafi. Bayan kuwa Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam yakan fara wani aiki ya bar shi, amma Annabi tun da ya fara iitikafi bai bar yinsa ba har ya bar duniya.

Imam Yahaya Ibn Muaz ya ce ban ga abin da ke kai mutun ga samun iklasi ba, irin mutun ya kebe shi kadai a masallaci yana tuna Allah. [109]

Akwai mutane bakwai da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce Allah zai sa su cikin inuwar alarshi ranar da babu wata inuwa sai ta Allah. Cikinsu akwai mutumin da ya kebe shi kadai ya ambaci Allah idanuwansa suka yin hawaye (kuka). [110]

FAIDOJIN  IITIKAFI

Maiitikafi yana samun rahama da gafara. Kadan daga cikin faidojin sa a kwai:

Samun Natsuwa.

Malaiku na nema wa mai iitikafi rahamar Allah da gafara kasancewar sa yana masallaci.

Allah na biya masa bukatunsa

Samun kusanci ga Allah. 

Samun lada mai yawa.

Koyi da Annabi.

Mai iitikafi na samun rahamar Allah.

Amintuwa daga fitina kasancewar sa a masallaci.

Samun damar karatun Al-kurani.

 Mika wuya ga Allah.

Neman tuba.

 Shiga inuwar Allah.


FADAKARWA:

Hikimar yin iitikafi ita ce kamantuwa da Malaikun Allah wajen shigar da lokacin ka gaba dayan sa wajen yi wa Allah daa da tsare zuciya daga shaawe-shaawe, da kusanci ga Allah wajen zama a dakin Allah (masalaci).

KWANAKIN IITIKAFI

Ana yin iitikafi ne kwana goma ko abin da ya yi kasa da haka. Mutum zai iya yin kwana biyu ko uku ko biyar ko shida ko kuma ya yi rana daya. Imam Malik ya ruwaito hadisi Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wa sallam ya yi iitikafi kwana goma. Malamai sun ce mafi karancin iitikafi shi ne kwana daya, ko kuma a ce rana daya, ko kuma dare daya, wato mutum yana iya yin na rana daya ko kuma dare daya.

Yazo a cikin Hiliyatul Ulama da alkafi na ibn Kudama cewa Idan ka yi niyyar yin iitikafi na rana (yini) daya, to zaka shiga masallaci kafin fitowar al-fijir. Hakanan wurin Ibn Kudamah Rana a lugga na nufin yini domin suna ne tsakanin fitowar al-fijir zuwa faduwar rana. [Almuguni]

LOKACIN SHIGA IITIKAFI

Ana shiga iitikafi ne kafin faduwar rana ko kafin fitowar alfijir sai mutum ya shiga masallaci. Yana kuma iya shiga bayan sallar subahi kamar yadda ya tabbata a hadisin Imam Bukhari.

SHARUDDAN YIN IITIKAFI

Dole ne wanda zai shiga iitikafi ya cika wadannan sharuddan: 

1. Dole ne ya kasance Musulmi 2. Mai hankali banda mahaukaci. 3. A mazahabar Abu Hanifa sai mutun ya balaga, amma sauran Malamai sun ce yaro ma zai iya yin iitikafi, wannan ita ce mazhabar Jumhuri, ita ce kuma magana ingantacciya. 4. Niyya: Dole ne a sami niyya yayin iitikafi. 5. Dole ne mutun ya kasance yana da tsarki banda masu haila da nifasi da mai janaba, wadannan ba sa yin iitikafi sai sun yi tsarki.

A BINDA MAI IITIKAFI YA KAMATA YA LAZIMTA

Mai Iitikafi yana da isashen lokacin wurin yin ibada, yana da kyau mai Iitikafi ya lazamci waddanna a bubuwa: 


Karatun Al-kuran

Yawaita yin istigfari

Yawaita yi wa Annabi Salati

Yawaita salloli na nafila.

Yawaita tuba ga Allah.

Yawaita sallatul tasbihi.


ABUBUWAN DA SUKA HALASTA GA MAI IITIKAFI.

1. Barci a cikin Masallaci.

2. Cin abinci acikin masallaci 

4. Sa turare da yin Kwalliya.

5. Yanke kunba da aske gashin mara da hammata, da yin aski.

6. Yin Bukka( gurin zama kebantacce) a cikin masallaci.

7. Kebance wurin zama na musamman wasu Malamai na ganin shi ne ya fi dacewa a ce kana da wuri kebantacce.

8. Zuwa da abin Salla.

9. Bin sallar gawa idan an kawo ta masallacin.

10. Daura aure idan an kawo daura auren masallaci.

11. Fita domin cin abinci in babu mai kawo ma shi, kuma ba zai iya dafawa ba.

ABUBUWAN DAKE BATA IITIKAFI.

1. Saduwa da iyali. (Jimai).

2. Ridda.

3. Zuwan jinin haila.

4. Haihuwa.

5. Hauka.

6. Fita ba tare da uzuri ba.

7. Maye: Idan mutum ya sha a binda ya ke sa maye iitikafinsa ya baci.

8. Suma.

9. Aikata babban laifi kamar zina da shan giya da karya da kazafi duk suna bata iitikafi.

10.Hirar banza mara amfani yana bata I,itikafi.

FADAKARWA ;

INDA AKE YIN IITIKAFI

Nana Aisha da ibn Abbas Allah ya kara masu yarda sun tafi a kan yin Iitikafi a masallacin jumaa, da Sauran mazhabobi guda hudu (4) duk sun yarda za a yi iitikafi a cikin Masallacin Jumaa. [Fathul Baari]

kuma wannan ita ce fahimtar sahabban Annabi baki dayansu banda Sayyidina Huzaifa da tabii Said bn Musayyib. [Fathul Baari]

Sayyidina Khuzaifa  yace sai a Masallatai guda uku (3): 1. Masallacin Kudus 2.  Massalacin Annabi 3. Massalacin Harami da ke Makka Kaaba. Kamar yadda sunan na Baihaki hadisi na 316  “Sayyidina Huzaifa ya zo masallacin ibn Masud ya ga ana yin iitikafi, sai ya ce wa ibn Masud ba ka hana su ba, kana kallonsu bayan ka san babu ittikafi sai a Masallatai guda uku: Masallacin Annabi da Masallacin Makka da Baitil Makdis (Kudus)? Sai ibn Masud ya ce masa mai yiwuwa sun dace kai kuma ka yi kuskure, kuma sun kiyaye kai kuma ka ka manta ne.

Wasu Malam suka ce Hadisin bai inganta ba, kuma yana da nakarar sanad da matan domin wanda ya ruwaito shi majahul hal ne. [Tarikul Bagdad 151 mujalladi na hudu (4)].

Wasu Malaman suka ce hadisin da ya ce a masallatai uku ya inganta amma yana nufin mafificin Iitikafi shine a masallatai guda uku Masallacin Annabi sallallahu alaih waalihi wasallam da masallacin Kudus da masallacin Makka. [136]

Hakan Hadisai da yawa sun zo suna bayanin halaccin yin i’itikafi a masallatan Juma’a.  

Baban Malami Alkali Abubakar ibnul Arabiy ya ce ‘’ mazahar Malikiyya a fili ya ke shine yin I’itikafi ako wani masallaci na Juma’a da sharadin in ana salloli biyar a cikinsa.

LAILATUL KADAR.

Daren lailatul Kadr ya fi watanni dubu alheri wanda ba wannan daren ba, haka Kur’ani ya bayyana alherinsa ya fi na shekara tamanin da wata hudu. Hadisai sun zo suna bayyana cewa ana samun wannan dare ne a cikin watan Ramadana ne.  Kuma ana samunsa a cikin goman karshen Ramadan. Ana samun wannan dare ne a cikin kwanukan mara, kamar daren 21,23,25,27,29, Amma an fi sa ran samunsa a daren ashirin da bakwai (wato bayan an kai azumi na ashirin da shida).

Hakanan ya zo a cikin hadisi Manzon Allah sallallahu alaihi waalihi wasallam ya ce ku neme shi (daren lailatulkadr) a dare na mara (Autara). An so mutum ya dage da ibada a cikin wannan daren ya raya sa da nauoin ibada, kamar karatun Alkurani da nafila, salati ga Annabi (SayyidinaA.W) da kuma zikiri, hakanan ma an so mutum ya umurci iyalinsa da yin ibada a daren su dukkansu. 

Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce wanda ya yi tsayuwar daren lailatul kadri Allah ya gafarta masa zunubansa wadanda suka gabata. [Bakhari]

Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya wa Nana Aisha (Allah ya kara mata yarda) wata addua da za ta rika karantawa a wannan dare. Itace:  اللهم إنك العفو تحب العفو فعف عنى

“Allahumma innaka afuwun tuhibbul afuwa fa’afu anni”. [TirmiZi].

A BINDA ALLAH YA KEBANCI DAREN LAILATUL KADR NA FALALA.

1. Allah ya saukar da Kur’ani a daren.

2. Allah ya girmama sha’anin daren.

3. Malaiku na sauka a wannan dare da rahama da   albarka da natsuwa.

4. Akwai gafarar zunubai.

5. Aminci da salama na sauka ga masu imani.

6. Ibada a wannan dare ta fi ibadar wata dubu a wani dare wanda ba wannan daren ba.

7. Daren ya fi wata dubu.

ALAMOMIN DAREN LAILATIL KADR

Lailatul kadr na da alamomi da ake gane shi da su. Wadannan alamomi sukan kasance ne cikin daren kansa:

Yanayi zai canza.

Za a ji iska mai dadi, Natsattsiya. [Ibn Khuzaima da Dayalisi]

Natsuwar zuciya da kimtsuwa.

 Farin ciki cikin zuciya da samun jin dadin ibada.

Za ka iya ganinshi (Lailatul Kadr) a mafarki kamar Yadda sahabbai suka gani

Rana zata fito ba zafi (in lokacin zafi ne). [Muslim]

Kashe garin daren rana kan fito

FADAKARWA:

Ba wai za ai mafarkin wani abu ba ne, a'a za dai a iya yin mafarkin ga shi ana ibada a cikin daren za ji karsashi wajen yin ibadarsa.

Wadannan su ne alamomin da ake gane daren lailatul kadr. Amma da ake cewa itatuwa zasu fadi su yi sujada, zaka ga rana a kasa, karnuka za su daina kuka, za a ga taurari a kasa, bai inganta ba. Allah ne Masani

ZAKKATUL FITR. (ZAKKAR FIDDA KAI)

Zakkatul fitr ita ce zakkar da ake fitarwa a karshen shekara, wato karshen watan Ramadana wanda ita ce Hausawa ke kira da zakkar fidda kai. Ita zakkatir fitr zakkar jiki ce da zuciya, kuma bai halasta ka dauke ta daga garinku zuwa wani garin ba, sai dai in ba wanda ya cancanta a garin. Kana iya fitar da ita a cikin azumi kwana biyu kafin a gama azumi kamar yadda Abdullahi bn Umar yake yi.

Zakkatul fitr Manzon Allah sallalLahu alayhi wa ali wasallam ne ya wajabta fitar da ita a karshen azumi. Ita zakkatul fitr ta wajaba ne a kan kowane musulmi, yaro ko babba, mace ko namiji mai yanci (Da) ko bawa. Maigida

shi ne ke fitarwa ga yaransa ko bayinsa ko matayensa ko wanda ke karkashinsa. [Wanda yak ciyar wa]

Ana fitar da ita ne daga shair, dabino, cukwi, sultu da sauran nauoin abincin da mutane ke ci.

Adadinta sai guda daya shi ne mudun Annabi sallallahu alaihi waalihi wasalam guda hudu kowane. Wata ruwaya ta ce rabin sai in zai fitar daga Jar alkama da ko kamhu.

Ba a ba da kudi, abinci a ke bayarwa kamar yadda sharia ta nuna, ba kuma a fitarwa ga jaririn da ke ciki. Wanda matarsa tahaihu kafin faduwar rana na karshen watan Ramadana ko kuma a ka yi masa rasuwa ko wani ya musulunta ko wani ya yi aure kafin faduwar rana za a fitar masu da Zakkar fiddakai, amma in bayan faduwar rana ne ba zai fitar masu ba.

Wanda aka tara masa Zakkatir fitr da yawa har ya ishe shi shima zai fitar da nasa zakkar daga ciki.

HIKIMAR FITAR DA ITA.

Yana daga hikimar fitar da Fidda kai kamar haka:

Tana tsarkake mai azumi daga kurakuran da ya yi a lokacin da ya ke azumi da kuma samar da abinci ga miskinai, don haka ne ma ba a ba da ta sai ga miskinai kawai. Bai halasta ba a ba wanda ba miskini ba.

Yana da kyau mutanen kowane gari su tara zakkarsu a wuri daya, sannan daga baya a rarraba ta ga wadan da suka cancanta. Musamman idan ana tsoran kin fitar da ita ga marasa cikakken sani a kan ta Manzon Allah sallalLahu alayhi wa ali wasallam ya yi haka, kuma ya sa Abu Hurayrah ya yi gadinta.

FADAKARWA

Badole bane ga miji ya fitar wa matarsa wanda bai riga ya kusance taba, ko ya aure ta ba ta riga ta tare gidansa ba. Hakanan, idan matarsa ta bijire masa lokacin Zakkatir Fitr ba dole bane ya fitar mata ba, ita zata fitar makanta ba mijinta ba sakamakon bijire ma miji.

Ko lokacinta ya wuce dole sai ka fitar da ita, ammaa a wurin wasu Malamai baka da ladan Zakkar sai dai ka sauke nauyin da ke kanka na wajibi kuma sai ka nemi gafarar ubangijinka.

2. AZUMIN NAFILA.

Azumin nafila, azumi ne da bawa ke azumta domin samun karin kusanci tsakanin sa da mahaliccin sa.

AZUMI GUDA SHIDA A WATAN SHAWWAL .

Ana son musulmi ya yi azumi guda shida a watan shawwal, Manzon Allah sallallahu alaihi waaihi wasalam ya ce idan mutum ya azumci watan Ramadan kuma ya bi shi da guda shida na shawwal kamar ya yi azumin shekara ne. Mutum zai iya yin su a jere in ya so, ko kuma ya yi su a rarrabe duk daya ne wannan ita ce fahintar Imam Ahmad bin Hambal. Shi kuma Imam Abu Hanifa da Imam ShafiI  suna ganin yin su a jere shi ya fi falala. Shikuwa Imam Malik Allah yayi masa Rahama yaki a reja Sittu Shawawal tare da Ramadana don gudun kada jahilai suga kamar an kara Ramadan ne.

Amma fa yana da kyau mu gane cewa wanda ake binsa azumi ba zai yi azumin shawal ba sai ya rama azumin da a ke binsa wannan ita ce Magana ingantatciya kamar wadanda suka sha sabo da haila ko haihuwa da sauransu sai sun rama na Ramadana sannan za suyi sitta sahawal haka ibn Rajab al-Hanbali ya fada.

AZUMIN TARA GA WATAN ZUL HIJJAH (RANAR ARFA)

Sunnace yin azumin ranar arfa, amma ga wanda yake gida banda mahajjaci, yin wannan azumi yana sa Allah ya gafarta mai zunubansa na shekarar da ta gabata da wacce za ta shigo.

AZUMIN GOMAN FARKO NA ZAUL HAJJ.

Nana Aisha Allah ya kara mata yarda ta ce Manzon Allah ya kasance yana yin azumin goman (Farko) na Zul Hajj. Wadannan kwanaki aikin alheri a cikinsu yana da tsananin Mahimmaci da falala a wajen Allah. Malamai sun kara wa juna ilimi a kan cewa, shin goman farkon Zhul-Hajj suka fi falala ko kuwa goman karshen Ramadan? Wasu sun tafi a kan cewa goman farkon Zul-Hajj sun fi, wasu kuma suka ce goman kashen Ramadan. 

AZUMIN TASUA  DA ASHURA.

Yin azumin Ashura yana sa a gafarta ma wanda ya a zumce shi zunubin shekara guda kamar yadda ya tabbata daga Manzon Allah. Hakanan Azumin Tasua

AZUMIN NAFILA A WATAN MUHARRAM

Yin azumi a cikin watan Muharram na daga cikin azumin da suka fi falala bayan watan Ramadan kamar yadda Muslim da Abu Dauda da Wasunsa suka Ruwaito.

AZUMI AWATAN SHAABAN.

Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya kasance yana yawaita azumin nafila a watan Shaaban kamar yadda aka ruwaito daga Uwar muminai Nana Aisha R.A.

AZUMIN ALHAMIS DA LITININ

Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya kasance yana yin azumin Alhamis da litinin inda ya nuni da cewa ana bijiro da ayyukan bayi ne a wadannan ranaku, inda ake gafarta wa muminai.

A wata ruwayar kuma yace Saboda a ranar aka haifeshi. Wanda wannan ya nuna cewa Annabi (SayyidinaA.W) yana girmama ranar haihuwar sa. Kuma wannan Hadisi ya nuna cewa maulidi yana da a Sali.

AZUMIN KWANA UKU A KOWANE WATA.

Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya nuna cewa duk wanda ya kasance yana yin azumin kwanaki uku a kowane wata kamar ya yi azumin shekara ne baki daya. An so idan mutum zai rika yin wannan azumi, to ya yi a cikin AYYAMUL BIDI wato Ranakun 13, 14, da 15, na kowane wata.

AZUMIN KWANA DAYA KA HUTA  KWANA DAYA

Wannan ma yana daga cikin azumin nafila masu falala. Kuma shi ne azumin Annabi Dauda wanda Manzon Allah ya nuna cewa shi ne mafi falalan azumi (Nafila) kuma mafi soyuwa a wajen Allah, kamar yadda ya tabbata.

KWANAKIN DA SUKA HARAMTA A AZUMCE SU

Wajibi ne musulmi ya guji yin azumi a wadannan ranaku masu zuwa. 

1. Ranar idi (Babban sallah da karamar Sallah).

2. Kwanaki ukun bayan babbar Sallah.

3. Ranar Jumaa kadai ba tare da hada ta da wata ranar a jere ba.

4. Ranar Shakka, (wato ranar da ake shakkar cewa tana cikin Ramadan ne ko shaaban.

5. Yin azumin kwanakin shekara baki daya.

6. Bai halatta mace ta yi azumin nafila ba tare da izinin mijin ta ba.

Allahu A'alamu.














Hajji

Gabatarwa: - Aikin hajji yana daga cikin rukunnan addinin musulunci kuma daya ne daga cikin wajibai da aka karfafa su a kan duk wani musulmi da ya samu ikon ziyartar kasa mai tsarki.

Allah Madaukakin Sarki yana cewa: “Kuma Allah ya dora ziyartar Dakin Ka’aba a kan mutane ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta, to lalle Allah mawadaci ne daga barin talikai”.

Harwa yau, ya zo cikin hadisi cewa: - Wanda har ya mutu bai yi aikin hajjin wajibi ba, kuma ba talauci ko rashin lafiya ko kuma hana shi zuwa aka yi bisa zalunci ba, to idan ya ga dama ya mutu bayahude ko banasare.

Hakika Ziyarar Dakin Allah mai girma sau daya ga wanda Allah Yaba iko Farillace ga Musulmi Da ko Diya, Baligi mai-hankali. 

Abin nufi da wanda Allah yaba iko shine: Wanda yake da guzirin da zai isheshi zuwa makka da karfin isa Makka, ya Allah da kafa ne ko bisa a bun hawa tare da lafiyar jiki. Anyi ummurni da sanya  Harami daga Mikati. 

Mikatin Mutanen Sham da Masar da Yamma (‘Yan Afrika) shine juhufatu, amma idan suka biyo ta madina to abin da yafi garesu su dauki Mikatinsu a inda mutanan Madina ke dauka wato “Zul-hulaifah”. 

Mikatin Mutanan Iraki shine “Zatu irkin”; Mutanen Yaman “Yalamlamu”; Mutanen Najad a “Karni” idan Mutanen Iraki, Yaman ko Najad suka biyo ta  Madina to wajibine sudauri Mikatinsu a “Zul-hulaifah”. 

Kamar yadda yazo a cikin  Bukhari hadisi na (133) da Muslim hadisi na (1182) 

عن عبد لله بن عمر رضي الله عنهما أنّ رسول الله ص قال "أهل المدينة من ذي الحليفة, وأهل الشّام من الجحفة, وأهل نجد من قرن" قال وبلغني أنّ رسول الله ص قال "ويهل أهل اليمن من يلملم"

Daga Sayyidina Abdillahi dan Sayyidina Umar﴾R.A﴿: Manzon Allah SAW yace: - “Mutanen Madina suyi harama daga  Zul-hulaifah, mutanen Sham kuma daga Juhfa, Mutanen Najad daga Karnul Manazil. Yace kuma labari ya riske ni cewa Manzon Allah (SayyidinaA.W) yace: “Mutanen Yaman suyi daga Yalamlam”.

Mai Hajji ko Umura zai dauki harami a karkashi Sallar Farilla ko Sallar Nafila. Yana cewa:

لبيك اللهم لبيك, لبيك لاشريك لبيك, إن الحمد والنعمة لك وملك لاشريك لك.

“Labbaykal Lahumma Labbayk, Labbaika Lashariy Ka Labbayk, Innal Hamda Wanni’imata Laka Wal Mulk Laashariy Ka Lak”.

Zai dauri niyyar abinda zai aikata na Hajji ko na Umura. An umurce shi da yin Wanka yayin daukar harami.


Rabe-Raben Aikin Hajji.

Aikin Hajji Nau'i Uku Sune:-

Nau'i na farko shi ne: Hajjin Tamattu’i.

Nau'i na biyu shi ne: Hajjin Kirani.

Nau'i na uku shi ne: Hajjin Ifradi.


Rukunan Aikin Hajji

Rukunnan Hajji Hudu ne (4)

Harama (niyya) 

Sa'ayi Tsakanin Safa da Marwa

Tsayuwa a Arafat 

Dawaful Ifada


Harama (niyya):- saboda fadin Manzon Allah (SayyidinaA.W) “Dukkan ayyuka basa karbuwa sai da niyya, kuma kowane mutum yana da sakamakon abin da ya yi niyya” [ Bukhari ne ya rawaito shi]

Sa'ayi Tsakanin Safa da Marwa:- saboda fadin Manzon Allah (SayyidinaA.W) : “Ku yi sa’ayi, hakika Allah ya wajabta muku sa’ayi” [Ahmad ne ya rawaito shi]

Tsayuwa a Arafat:- saboda fadin Manzon Allah (SayyidinaA.W) “Hajji shi ne tsayuwar Arafa” [Tirmizi ne ya rawaito shi]

Dawaful Ifada:- saboda fadin Allah Madaukakin Sarki : “Su yi dawafi ga daki da dadde” . (Al-hajj: 29)

Fadakarwa : Wanda ya bar wani rukuni daga rukunan hajji, to hajjinsa bai yi ba, har sai ya zo da shi.

Wajiban Aikin Hajji.

Aikin Hajji ya na da wajibai kamar:

Yin harama daga mikati, Kamar yadda ya gabata.

Tsayuwar Arfa har rana ta fadi ga wanda ya zo da rana:- saboda Annabi (SayyidinaA.W) ya tsaya har zuwa faduwar rana. Da kuma hadisin Imamu Tirmizi kamar dai yadda ya gaba ta asama.

Kwana a Muzdalifa:- saboda Manzon Allah (SayyidinaA.W) ya kwana a cikinta, ya ce, “Ku riki yadda ake aikin hajji a wurina, don ni ban sani ba, watakila ba zan sake haduwa da ku ba bayan wannan shekara” [Ibnu Majah ne ya rawaito shi] 

Kuma saboda Manzon Allah ya yi wa masu rauni izinin tafiya bayan dare ya raba, sai wannan ya nuna cewa kwana a Muzdalifa dole ne. sannan kuma Allah ya yi umarni da ambatonsa a wurin da ake kira “Mash’arul Haram” a Muzdalifa.

Kwana a Mina a dararen kwanakin yanyana: - Saboda abin da ya tabbata daga Annabi (SayyidinaA.W) na cewa “Ya yi rangwame ga masu kiwon dabbobi kada su kwana a Mina” [Abu Ya’ala ne ya rawaito shi a littafinsa «Musnad»] Wannan ma yana nuna cewa wajibi ne a kwana a Mina

Jifan wuraren jifa uku:- saboda fadin Allah Madaukakin Sarki

واذكروا الله فى ايّام معدودا ت 

“Ku ambaci Allah a cikin wasu kwanaki kididdigaggu” (Al-bakra 203)

Kwanaki kididdigaggu su ne kwanakin ‘yan yana, Jifa yana cikin ambaton Allah Madaukakin Sarki, saboda Annabi (SayyidinaA.W) ya ce, “An sanya dawafi ga dakin Allah da sa’ayi tsakanin Safa da Marwa da jifa don tsayar da ambaton Allah” [Abu dawud ne ya rawaito shi]

Aske gashin kai gaba daya ko saisaye: - Saboda fadin Allah Madaukakin Sarki : لتدخلن المسجدالحرام إنشاء الله ءامنين محلقين رءوسكم ومقيرين لاتخافون

“Tabbas zaku shiga masallacin harami, in sha Allahu kuna masu aske kanku gaba daya ko kuna masu saisaye” (Al-fathu : 27).

Dawafin ban-kwana: -Saboda abin da ya tabbata daga  Abdullahi dan  Abbas Allah ya yarda da su yace, “An umarci mutane ya zama karshen lamarinsu ga Makkah dawafi ga Ka’abah, sai dai an yi rangwame ga mai haila” [Muslim ne ya rawaito shi]


Sunnonin Aikin Hajji

Duk abin da ba rukuni ko wajibi ba, to sunna ne, kamar abubuwan da za su zo :

Wanka yayi sanya Ihrami

Yin ihrami a cikin kwarjalle da mayafi farare.

Yin talbiyya da daga murya da ita.

Kwana a Mina daren ranar Arafa

Sumbatar bakin dutse. (Hajarul aswadi)

Yaye kafadu yayin yin (dawafin kudumi) ko umara, shi ne sanya mayafi karkashin hammatar dama

Yin sarsarfa a zagayen ukun farko na (dawafin kudumi) ko umara.

Yin dawafil kudumi ga wanda yake kirani, da mai yin Ifradi

Fadakarwa akan Sunnonin Hajji: 

Wanda ya bar sunna daga cikin sunnoni aikin hajji, babu komai a kansa, hajjinsa ya inganta.










AURE:

Aure sunna ce daga cikin sunnonin manzanni wadda Allah ta`ala yayi umarni da ita.ma`anarsa:wani kulli ne dake halatta jin dadi tsakanin namiji mace abisa tsarin wasu dokoki. Aure a musulunci yana da rukunnai hudu:

Waliyyi 2. Shedu
3. Sadaki 4. Siga.

Daga cikin aure akwai wanda yake batacce kamar:

Auren Mutu`a: shi ne mutum yayi yarjejeniya da wata mata akan ya aureta amma zuwa lokaci zasu rabu.Kome tsawon lokacin wannan haramun ne kamar yadda ya tabbata a Hadisin ma`aiki (SayyidinaA.W).

Auren Tsoka Da Tsoka (Shigar): Shine mutum yacewa wani aura mani diyarka, sai yace masa ‘da sharadin kaima zaka aura mani taka’ to wannan ko da sadaki ko baba haramunne.

Aure Cikin Idda: Idan ko har ya sadu ita, ba aure tsakaninsu har abada.

Auren Kishin Wuta: Tirmizi ya ruwaito Annabi (SayyidinaA.W) yace: Allah ya tsinewa  mai kashin wuta da wanda ake kashe mawa kuma a sani wutar bata mutu ba.

Aure Ba Waliyyi: Shine auren da aka yi batare da waliyi ba. Domin Walicci na daya da ga cikin rukunnan Aure.



SAKI

Saki shine warware igiyar aure da wani lafazi bayyananne ko kinaya.Anayin saki ta hanyoyi daban-daban. Sai dai baya halatta mutum ya saki matarsa tana haila ko biki, amma idan ya sake ta ahakan ta saku, shi kuma ya aikata bidi`a.

TAFARKIN SUNNA A CIKIN AURE

Shehu Usman dan Fodio ya fada a cikin littafinsa Ihya`Ussunna: Lallai hanyar sunnah ta Muhammadiyya it ace:

Mutum yayi niyyar raya sunnar Annabi SAW da wannan auren nasa.

Kuma wanda keda halin yin aure to yayi. 3. Kwadayin mace ma`abociyar addini.

Mutum ya kiyayi neman auren mace bayan ta fidda Miji.

Iyaye su kiyaye hana mace ta koma gidan Mijinta.

Walima. Saboda fadarsa Sallallahu alaihi wasallam: kayi walima koda da Akuya ce.

TAFARKIN SHEDAN A CIKIN AURE

Shehu Usman dan Fodio ya ambata a cikin Ihya`Ussunna cewa: Yana daga abinda mutane suka kirkira a fagen aure “Walimar da take Hade da barna” wannan bidi`a ce haramtatta a haduwar malamai. Kwarin azaba ya tabbata ga mijin da wanda ya taimaka masa.Kuma babu albarka a cikin wannan auren. Wannan magana yana yin ta ne game da gamin dambizar Maza da Mata awurin biki ko akwai DJ ko babu.Akwai kuma hakkin shimfida da wasu mata keamsa. Shima bidi`a ce haramtatta a haduwar malamai.

Wannan Magana yana yin ta ne game da matan da mazansu ba zasu kwantawa da su ba har sai sun basu wani abu. To Allah ya sawwake.

IDDAH

Idda wadansu kwanakine da matar da ta rabu da mijinta take zama a cikinsu kafin ta sake wani auren.

AMFANIN YIN IDDA/DALILAN YIN IDDA

Tana bada damar yin sasanci tsakanin ma`aurata, idan saki daya ne ko biyu.

Don a gane matar tana da ciki koko, don magance yan tsugunne-tsugunnen waye babansa mijin farkon ko na biyun.

IRE-IREN IDDA:

Daga cikin nau`o`inta akwai:

Wadda mijinta ya mutu wata 4 da kwana 10.

Yarinyar da bata fara jini ba, da kuma tsohuwar da ta girmi jini, wata (3).

Matar da ta ke yin jini za ta yi jini 3.

Mai ciki (har sai ta haihu).

Wadda aka saki kafin tagama iddar sai mijin ya mutu (Sai ta koma iddar wadda Mijinta ya Mutu, wata 4 da kwana 10) kuma zata gajeshi.

Wadda take Idda da jini sai jinin ya dauke dalilin rashin lafiya ko waninta. (Zata jira jinin ya dawo ta cigaba da lissafi). Idan kuma ba`asan dalilin daukewarsa ba (zata lissafa shekara guda sanna ta gama). Ya zama kenan wata Tara 9 adadin ciki wata Uku 3 na idda. Idan kuma ya dawo sai ta cigaba da lissafi da shi.

Wadda an daura aure Mijin bai je in da take ba sai ya mutu (babu idda akanta, kuma bata da sadaki, amma zata gajeshi.

HAKKIN MIJI DA KUMA LADAR AURE:

Wannan Babi zaiyi Magana ne a kan a bin da Allah ya shara anta na biyayyar da Mata za suyiwa Mazajen su. Da kuma ladar da Allah ya tana dar masu.

Annabi (SayyidinaA.W) yace: “farkon abinda za`a fara tambayar Mace ranar alkiyama Sallarta sai Mijinta ta zauna da shi”. 

Awata ruwayar Annabi (SAW) yace; “Allah baya duban Matar da bata godewa Mijinta, kuma bata wadatuwa da abinda ya kawo”. 

Kuma Yace;  “idan Mace ta fito daga gidan Mijin ta bada izininsa ba Mala`iku zasu  ta tsine mata har sai ta dawo”. Innalillahi waInna Ilaihiraji`una.

Sayyiduna Aliyu (R.A) ya tambayi Mai Dakinsa Nana Fadimatu (RTA) ‘Yar Ma`aikin Allah (SAW)’ Me yafi alheri ga mace? Sai tace  “kar ta ga Maza kar su ganta”. 

Annabi (SayyidinaA.W) yace:  “Duk Matar da ta cutar da Mijinta da harshenta Allah baya karbar Sallar farillarta bare nafilarta, ko wani kyakkyawan aiki nata,  har sai ta nemi yafiyarsa koda ta azumci yini ta sallaci dare...”. Kuma yace: “Duk Matar da bata tausayawa Mijinta ba, ta sa shi abinda yafi karfinsa Allah baya karbar aikin alherinta…”. Shehu Abdullahi dan Fodio kanen Shehu Usman dan Fodio ya fada a littafinsa Kitabul Mawa`izi:  Aliyu ya ruwaito cewa Ma`aiki (SayyidinaA.W) ya shigo wurinmu sai  Nana Fadimatu tace ya babana bani labari game da matar da ta dubi mijinta cikin fushi? Sai yace “Ya Diyata, Allah zai rubuta mata zunubai yawan taurari,kuma duk matar da ta cewa mijinta;  “Ni Ban Taba Ganin Alheri Wurinka Ba” Allah ya haramta mata ni`imar Aljanna”. Ya Fadimatu, duk matar da tayi wa mijinta gori, tace kaci dukiyata, kasa tufafina, ba zataji kamshin Aljanna ba, kuma ba za`a karba addu`arta ba har sai ya yafe mata. Duk matar da take cutar da mijinta da harshenta, Allah zai maida harshenta tsawon zira`i (70) mazauninta kuma yana cikin wuta. Duk matar da take da dukiya, sai mijinta ya bukaci wannan dukiyar, sai ta hana shi, Allah zai maida fuskarta baka ranar alkiyama.(ku kuma maza kuji tsoron Allah karku zalunci matanku. Duk matar da ta saci koda ‘kwaya’ a gidan mijinta, Allah baya karbar sallarta bare azuminta. Duk matar da ta ci amanar mijinta ga dukiyarsa ko kanta; mala`iku zasu tsine mata kullum sau (70). Duk matar da ta shafawa kan mijinta man shafawa, Allah zai shayar da ita daga koramun Aljanna, kuma Allah ya saukake mata magagin mutuwa. Idan miji ya cewa matarsa ‘Na Yarda Dake’ ya fiye mata ibadar shekara (60). Wadda ta shayar da mijinta wani abin sha, tai masa hidima har ya sha, ladar wannan ta fiye mata ibadar shekara. Idan ta kawo mashi abinci don biyayya ga umarnin Allah, zata samu lada ladar ‘Rahmatu matar Annabi Ayyuba da Maryam bintu Imran’ zata zama kawarsu a Aljanna, kuma za`a tada ta cikin ayarin ‘Nana Fadimatu bintu Muhammadin (SayyidinaA.W). Duk Matar da ta shimfidawa mijinta wata shimfida, Allah zai bude mata kofofin aljanna haske yarika shiga kabarinta, kuma zata rika ganin mala`iku (60) ko wace rana. Duk matarda ta debi wani kaso cikin sadakinta taba Mijinta,Allah zai bata ladar `yanta baiwa.Duk Matar da ta boye sirrin Mijinta Allah zai sanyata cikin Matan Aljanna.A Cikin Littafin ‘Algunya’ shafi na 77 a wani dogon hadisi na ‘Uwar Muminai Maimunatu’ “Matar dake biyayya ga Mijinta tana samun ladar shahidi Dubbu daya kullum.

HAKKIN YAYA AKAN IYAYE

Yaya na da hakki akan Iyayensu mai tarin yawa wanda a wannan zamanin Iyaye suna ganin wannan ba komai bane kamar Allah ma ba zai tambayesu ba. Wannan abu ne mai matukar hadari.Imamu Tirmizi ya ruwaito Ma`aiki (SayyidinaA.W) yace: Uba ba zai wa dansa kyauta ba wadda tafi kyakkyawar tarbiyya.

Tarbiyya ana bada ta ta hanyoyi daban-daban kamar bada tsoro, aibantawa, bugu;ba mai illa ba, fadakardasu dukkan wani abu mai amfani da mai illa.Sayyiduna Abu Zarrin (RA) yace: “wata rana muna tare da Annabi (SayyidinaA.W) yana sanar damu hadisansa,  (RA) Alhasan da Alhusain (RA) suna wasa bisa bayansa, bayan ya gama sai yace ku sauko;sai suka hango babansu sai suka saukadon tsoronsa. Sai Annabi yace masu ya akai? Sai suka ce babanmu muke tsoro. Da isowarsa sai ya bugesu yace ladabi ya dace daku.Sai Annabi yace ya Aliyu kada kayi masu tsawa domin yan gatanane. Sai yace munji munbi ya Rasulallahi. Sai ga Mala`ika Jibrilu (A.S) ya sauka yace: ya Annabin Allah, Allah yace  kabarshi ya tarbiyyantar dasu. Ku cida ya yanku, ku kyautata sunayensu,  ku tsarkake jikinsu, za`a azurtaku da cetonsu. Da Annabi yaji haka sai yace: ya ku Musulmai, wanda Allah ya azurtashi da Da, ya wajaba ya tarbiyyantar dashi da ilimantar dashi. Domin wanda ya ilimantar da dansa kuma ya bashi tarbiyya Allah zai azurtashi da cetonsa, wanda yabar dansa jahili, duk zunubin da ya aikata yana kansa. Haka yake cikin littafin Tanqihul Kauli. To idanwadannan jikokin Annabine, Allah yace Iyayensu su basu tarbiyya, naka kuma jikokin waye. In har akwai wanda za`a seta daga sama bayan Annabi, to bai wuce tsokar jikinsa ba.Alhamdulillahi Iyayenmu da Malaman mu Allah yayi masu sakayya ta alheri alfarma Ma`aiki (Sayyidinaa.w).

Imamu Abu-Dawuda da Imamu Nisa`i sun ruwaito, Ma`aiki (Sayyidinaaw.) yace:ko wane yaro jingine yake da ragon sunansa, ana yankashi ranar 7 a yi masa suna, a yi masa aski. Cikin (Minhajul Muslim) na Abu-bakr Jabir Aljaza`iri, babi na 4 fasali na 14 yace: “Anso a radawa yaro suna ranar 7 a kuma kyautata sunansa… kuma ayi masa kiran sallah kunnen dama, ayi masa ikama kunnen hagu”. Kyautata suna shi ne zaba masa suna mai asali, daga sunayen Allah (Abdullahi, Abdurrahman, Abdurrahim)ko na Annabawa ko na wasu Mutanen kirki. Ba sunayen zamani ba na ‘yan-kanti’. ‘Da’ yana sanin darajar Iyayensa ne idan sun bashi tarbiyya ta gari. Sai ayi ta zagin yara akan sun yi wata rashin kyautawa, alhali kyalesu akayi su yiwa kansu tarbiyya, ko abarsu da malaman Islamiyyarsu, wanda hakan bai yiwuwa sai da taimakon Iyaye.

HUDUBA TA KARSHE

Zaman aure hakuri ake bukata a cikinsa, wannan dole ne ba makawa, tunda dole ne wata rana za ta yi maka laifi, kuma kaima wata ranar zaka bata mata rai, shin idan ba`ayi hakuri ba, wannan zaman zai kai wani lokaci kuwa? A duba da kyau. Dukkan abinda muka ambata a sama na hakkin miji akan matarsa, to itama tana da wannan hakkin akansa, ba sai an sake wani lissafi ba na daban.

ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN








INDA AKA CIRATO    
                       (الكتب المراجعة)


1. Muttamalik

2. Sitta Sihahi

3.Algunya (Suldaa nil Auliya'i Sheikh Abdulkadir Jilani Qaddasallahu Sirrahu wa ardahu).

4. Attamhid na ibn AbdulBar

5. Ladaa'iful Maarif

6. Ihyaa'us Sunnah (Shehu Usmanu bn Fodio)

7. Sahihu Targhib wattarhib Imamul Munzir

8. Tarikul Bagdad mujalladi na hudu (4)

9. Tafsirul Ibn Kasir

10. Fiqhu ala mazahibul Arbaa

11. Nayl Al-Awwatar (ash- shaukhany)

12.. Kitabul Mawa'iz. (Sheikh Abdullahi bn Fodio)

13. Bugyatul Muslim wa kifayatul wa'izina walmuta'aziina (Ashshaikh Alhaji Usmanu ibn Abi Bakara)

14. Abu zayd al-Kirawani (Risala)

15. Ladiyful minani

16. Al-Akhdariمختصر الأخضري                                                                                          

17. Hallul-Masa'il.                                                   حلُّ المسائل في شرح مختصر الأخضري     

18. Iziyyahالمقدمة العزية                                                                                                      

19. Kawaniynul-Fikihiyyah         القوَانِينُ الفِقهِيَّة                                                                  

Dahawi

Darulkudini

Abu Daud 

Ibn Majah

Bukhari 

Muslim

Ahmad 

Baihaki 





Comments

Popular posts from this blog

📘 Sufism in Islam and Its Contributions to the Muslim World

  Part 5: Global Impact & Conclusion 🔹 12. Contemporary Sufism and Global Influence 🌐 Digital Revival: Sufi teachings spread via online zawiyas, YouTube, and apps. Institutions like Zaytuna College and Cambridge Muslim College promote classical spirituality for the modern age.

Falalar Faɗin “Subhanallah” Kullum

 Falalar Faɗin “Subhanallah” Kullum Da Sunan Allah, May Rahama, May Jin ƙai Gabatarwa Say “Subhanallah” when you read the Musulman. Wannan kalma na nufin girmama da tsarkake Allah daga duk wani nakasu. Yayin da Musulmi ya faɗi Subhanallah, we have no amincewarsa da cewa Allah cikakke ne a dukkan siffofinsa da ayyukansa. Wannan takaitaccen bayani yana bayyana dalilai na addini, hadisan Manzon Allah, peace be upon him, da ayoyin Alƙur'ani da ke nuna muhimmancin faɗin “Subhanallah” in the kullum.

The Benefits of Reciting the Qur’an Daily

 The Benefits of Reciting the Qur’an Daily Introduction Reciting the Qur’an daily is more than a routine; it's a spiritual connection with Allah. It strengthens faith, offers guidance, brings peace to the heart, and improves understanding of Islam. Each letter recited earns boundless rewards.